NASABARSA Asalin alu musharraf Asali alu musharraf Zaaen
NASABARSA � �
Asalin alu musharraf Asali alu musharraf Za~a~~en gidane daga cikin gidajen hanzalah, ita kuma hanzalah za~a~~ace daga cikin }abilar banu tamim. � Wannan gida na Alu musharraf sun kasance fitattu wajen ilmin Addini; don kuwa daga kakannin sheikh na tara har zuwa kansa su ke ri}e al}alancin garin uyainah. � Asali sun zauna ne a garin ushai}ar dake yankin Najd (yankin Riyadh saudi arabia) daga bisani suka }aura zuwa tsakar yankin Najd. � Alkhairi da Allah s. w. t ya shimfi]awa wannan zurriyya bai tsaya ba har izuwa wannan lokacin; don kuwa ko yanzu ‘ya’yan sheikh ke jagorantar al’amuran addini a kasar musulunci ta saudi; bisa cancanta. �
Banu Tamim � � bani tamim gidane daga cikin manyan gidajen ‘ya’yan Adnan, shiko Adnan yana daga cikin zurriyyar Annabi Ismail ]an Ibrahim alaihimassalam. }abilar banii tamiim nada falala masu yawa, daga ciki ankar~o hadisi daga Abu hurairah Allah ya yarda dashi yace: bazan gusheba ina }aunar banii tamiim saboda abu uku da naji daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam; naji yana cewa : banii tamiim sune mafi tsananin alummata akan dajjal(wato dajjal zai sha ba}ar wuya awajensu kuma bazai samu damar ~atar da suba), sannan sadakarsu tazo sai Annabi sallallahu alaihi wasallam yace wannar itace sadakar danginmu(sai ya danganta kansa dasu), sannan akwai wata yarinya daga cikinsu a wajen Aishah sai Annabi sallallahu alaihi wasallam yace ki ‘yantata domin ita tana daga cikin ‘ya’yan Ismail. bukhariy da muslim suka ruwaitoshi.
MUHAMMAD BIN ABDULWAHAB ‘ ‘YA’YANSA HAIHUWARSA � � An haifeshi a birnin uyainah(Arewa maso yammacin riyadh a shekarar 1115 H, wato 1703 M, anan kuma ya girma. Ya kasance mai kaifin basira da fasaha, ya haddace al}urani baikai shekara goma ba. � � Yana da ‘ya’ya bakwai, sune: hassan, hussain, abdullah, abdulaziz, ibrahim, aliyu, fa]imah. Kaga cikin ‘ya’yansa akwai raddi ga ‘yan shiah (rafidhah) da sukayi masa sharri cewa baya son ahlul baiti; domin shida daga cikinsu duk sunan ahlul baiti ne yasanya musu.
Neman iliminsa � Ya rayu cikin ilmi, nemansa da bayar dashi, kamar yadda ya tashi gidan karatu domin dukkanin kakaninsa malamaine. �Ya balaga bai wuce shekara 12 ba, kuma a wannan shekara babansa yai masa aure hakan ya temaka masa mati}a wajen karatu; tarashi da bayarshi.
Tafi ya rsa neman ilmi � Tafiyarsa ta fari ta kasance zuwa hijaz ne(wato makkah da madinah). � A can Hijaz yayi karatu a wajen malamai da dama ciki akwai fitattu guda biyu sune: � Sheik Abdullah bn Saif Annajdiy: ya bashi ijaza(certificate) ta hanya biyu; 1 -zuwa sheikhul Islam Ibn taimiyyah har izuwa Imam Ahmad bn hanbal, 2 -Ibn }ayyim zuwa Imam Ahmad. � Sheik muhammad hayat assundiy.
Tafiyarsa basra domin neman ilimi � Ya isa basra a shekara ta 1136 H, ya samu ilimi mai yawa anan. � Malamin da yafi lazimta anan shine: sheik Muhammad Almajmuiy. � Sheik duk tafiye-tafiyensa sun ta}aitanene tsakanin wurare uku: hijaz(makkah da madinah), Ahsaa, da kuma Ira}(Basrah).
�Wa]anda ambatonsu ya gabata da kuma: �Sheik Muhammad Alahsaiy. � Babarsa, da kuma Babansa, da Baffaninsa. �Ya kasance daga cikin malaman da suka fi kowa lazimtan malamai a zamaninsa da kuma ]aukan ilmi a wajensu. �Ya kasance akan mazhabar Hanbaliyyah.
Littattafansa da A{idarsa � Daga cikin littattafansa akwai: � Kitabuttauhid. � Usulul thalatha. � Kashfushshubhat. � nawa}idul islam. � Usulul iman. � Da wasu littattafai masu yawa. � A}idarsa itace a}idar Ahlussunnah wal jamaah. � Domin }arin bayani ka koma littafin mu mai suna: me kasani gameda Sheikh Muhammad bn Abdilwahab.
Abubuwan da yake karantarwa a majalisansa Rayuwarsa ya bayar da itane ga ilimi, ya kasance a majalisansa ya kasa karatuttukansa gida hu]u: � 1 - cikin asalin addini(Tafsirin LAILAHA ILLALLAH, asula uku da saninsu ya wajaba akan kowane musulmi, (sanin Allah, manzonsa, da addinin musulunci da dalilansa). � 2 - Bayyana }aidojin musulunci daga wajibansa da hukuncensa da haninsa. � 3 - Karantar da mutane matsayin manzon Allah, da kuma ha}i}anin abun da yayi kira akai. � 4 - Tabbatar da tayarwa bayan mutuwa (tashin }iyama) da dalilai da hujjoji. �
� � Ya gama tafiye-tafiyensa a shekarata 1140 H, daga nan ya lazimci bincike da kuma bayar da ilmin da Allah ya azurtashi ya tara a tafiye-tafiyensa na neman ilimi. Yayinda ya dawo daga karatu da ya zagaya nema, sai ya samu mahaifinsa ya }aura daga garin uyayinah zuwa Huraimila saboda haka shima ya tafi wajen mahaifinsa, a wannan garin ne kuma ya fara daawarsa ta kawo gyara cikin abubuwan da wasu ma~arnata suka cusa cikin addini. Bayan rasuwar mahaifinsa ne wasu daga cikin ‘yan bid’ah wannan gari suka nemi kashe sheikh wanda hakan yasanyashi hijra zuwa mahaifarsa uyainah. Daga uyainah kuma yai hijrah zuwa garin Dir’iyyah inda ya ha]u da sarki Muhammad ]an saud suka ci gaba da kira zuwaga Allah, wanda sababin wannan daawa Allah ya samar da daular saudiya.
� Babban abin da Sheikh ya yi kira akai shi ne: � 1 - Ka]aita Allah da ibada, � 2 - Ya}ar shirka da nau’o’inta da � 3 - Rushe bidi’o’i, � 4 -Aikata umurnin Addinin musulunci a cikin shari'o’i da kuma ma’amala. � Wa]annan abubuwa su ne abubuwan da annabawa suka mayar da hankali a kansu, da magabata managarta, don haka da'awarsa ba ta sa~awa ta wa]annan manyan bayin Allah ba.
Ha}i}anin Daawarsa � Ha}i}a sheik Muhammad bn Abdulwahab ya tashi cikin lokaci da shirka da bidioi suka cika duniya sakamakon ta~argazar da Sufaye da Rafidha sukayi a cikin Addinin musulunci na canje–canje da kuma }are–}are. Lura da haka yasa sheik ya fara kira Zuwaga Allah tare da inkarin dukkan Abunda ake aikatawa wanda ya sa~awa shari’ah na daga shirkoki da bidioi da sauransu. ya fara kira zuwaga gyara da kuma komawa zuwa ga addinin musulunci kamar yadda manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yazo dashi.
Yace � Sheik yace : ina labarta muku cewa Ni : -ina godewa Allah A}idata da Addinina da nake bautawa Allah dashi; shine mazhabar Ahlussunnah Walja’maah wanda akan sane imaman musulunci suke kamar imamai guda hudu(Imam Abu hanifa, Imam Malik, Imam Shafi’i da kuma Imamu Ahmad) da kuma mabiyansu har izuwa ranar }iyama, kuma ni na bayyanawa mutane tsarkake Addini ga Allah, na kuma hanasu ro}on Annabawa da mamata (daga salihai) da wasunsu, da ha]asu da Allah a cikin Abinda ake bautawa Allah dashi, shi ka]ai na daga yanka, bakance, tawakkali, sujadda da wasun wa]annan Abubuwa wa]anda suke ha}}in Allah ne shi ka]ai; wani mala’ika makusanci bai isa yai tarayya dashi a cikiba haka kuma wani Annabi da aka Aika (manzo), wannan shine Abinda manzanni sukai kira akai tun daga farkonsu har izuwa }arshensu, kuma akanshi Ahlussunah Wal jamah suke.
Masu fa]a da daawarsa � � � Suko masu cin zarafin sheik sun kasu gida uku. 1 - Masu fa]a dashi da daawarsa domin idan sunnah ta kafu matsayinsu zai fa]i a idon shuwagabanni da sukewa }arerayi ko kuma ]alibansu da suka ri}esu iyayen giji koma bayan Allah. 2 - Sun jahilci daawar : wa]annan ~angaren basu san menene gaskiyar daawar ba, suna fa]a da itane akan jahilci. 3 - Son zuciya : wannan ~angaren kuwa shine yafi ]iban malamai da mabiyansu, ya kuma fi zamar da }afar wanda ya ru]u, domin da yawa zaka samu mutum yasan cewa gaskiyace amma sai son zuciya ya hanashi bayyanawa. Muna fatan kada Allah ya sanyamu daga cikin masu fa]a da gaskiya!.
DALILAN DA SUKA TAIMAKA WURIN YA[UWAR DA’AWARSA � � � � � Da'awar sheikh Muhammad ibn Abdul. Wahhab ta shiga ko'ina cikin duniya, kuma akwai abubuwa da dama da suka sa ta ya]u haka ko'ina a ban }asa. Ga wasu daga ciki: Tushenta: Kasancewarta an gina ta akan Littafin Allah da sunnar manzon Allah (S. A. W). [abi’ar da’awar: Kasancewarta a fayyace ga duk mai son gaskiya, kuma ta yi daidai da lafiyayyen hankali (wanda ya ku~uta daga dafin ~ata da son zuciya) domin kuwa kira ne zuwa ga asalin addinin musulunci wanda Annabi Muhammad (S. A. W) ya zo da shi. Ma'abocin daawar da kuma kyakkyawar niyyarsa: Akwai alamar lkhlasi a aikin wannan bawan Allah, sannan }o}arinsa da dagewarsa wurin tabbatar da addinin Allah da harshensa da takobinsa ya sa Allah ya }arfafi da'awar. {arfin mulkin Al Saud: Sun bayar da gudunmawa mai yawa a halin rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa a fagen taimakon addinin Allah. Malamai: Malaman sunnah na cikin Saudiyya da wajenta sun yi aikin yabawa wurin isar da sa}on Allah da wannan da'awa ta }unsa. Lokacin Da'awar: Kasancewar mutane a hali ma}untaci da kuma bu}atuwarsu da a kawo gyara cikin abin da mutane suka ~ata a addinin Allah, da kuma yin da'awar gyara a wannan lokaci, ya sa da'awar ta samu kar~uwa. Wurin hajji: shigar yankin Hijaz }ar}ashin mulkin Saudiyya a shekara ta (1218 H-1226 H), da kuma dawowarta bayan ku~ucewa a shekara ta (1343 H) ya taimaka matu}a wurin fahimtar da mahajjata ha}i}anin wannan da'awa. Kasuwanci: Ala}ar kasuwanci ta taimaka matu}a wurin ya]a wannan daawar mai albarka.
Sakamakon Daawar � Abune sananne ga duk mai neman gaskiya cewa daawar sheikh Muhammad bn Abdulwahab ta kawo gyara da ci gaba na gaske dama }ara ha~aka ilmin addini tun daga }arnin da ya rayu har izuwa yau. � Sababin daawarsa da dama daga cikin wa]anda suka jahilci sunnan Annabi sallallahu alaihi wasallam sun fahimceta. � Sababin wannan daawa tashi an samu kafuwar daula musulma mai bayar da kariya ga addini da kuma harami guda biyu (makkah da madinah) a daidai lokacin da ake mati}ar bu}atan hakan.
Ya gamu da rashin lafiya a watan shawwal, sannan Allah ya kar~i rayuwarsa a wannan watan; shekarata 1206 H, daidai da 1792 M, yana da shekara 91. ya bar zurriya mai albarka. Allah ya gafarta masa.
� Rubutawa da tsarawa : Jaafar Saad (Abu � Domin samun cikakken tarihin wannan Muhammad). malamin ka nemi littafina mai suna : me kasani gameda sheikh Muhammad bn Abdulwahab; wanda nan kusa inshaallah zai sauka a site dina. � Domin samun rubuce-rubucena kai tsaye kana iya garzayawa zuwa ga blog dina : http: //bensaadgombe. wordpress. com � Ko ka rubuta min email akan : binsaad 12@yahoo. com � Da fatan duk wanda wannan abu ya isa gareshi bazai gaza ba wajen isar dashi ga waninsa. � 1434 H2013 M (ALMADINAH ALMUNAWWARAH).
- Slides: 20