Cutar Coronavirus 2019 COVID19 Abubuwan da ya kamata
Cutar Coronavirus 2019 (COVID-19) Abubuwan da ya kamata ka sani Version 3. 0 Rashin daukar Alhaki: Wannan bayanin an haɗa ne domin ilimintarwa kawai. Kuma ba don maye gurbin shawarwarin likita ba. Idan ka na da tambayoyi ko damuwa game da batun da aka yi bayani anan, dan Allah a nemi shawara daga masana. © 2020 AEA International Holdings Pte. Ltd. An kare haƙƙin mallaka.
Abubuwan da suke haddasa ciwon huhu mai tsanani coronabirus 2 (SARS-Co. V-2) COVID-19 • SARS-Co. V-2 sabuwar ƙwayar cuta ce. • Farkon mutanen da suka kama shi na tare da nimoniya a garin Wuhan, a ƙasar China, a Disamba 2019. • Wataƙila ya fara da dabbobi amma yanzu yana yaɗuwa tsakanin mutane. • Tunda ƙwayar cutar sabuwa ce, muna ƙara ilimi a kowane lokaci, kuma abubuwan da muka sani na iya canzawa. 2
Matafiya suka kai ƙwayar cuta zuwa wasu ƙasashe • Ƙasashe da yawa sun gano ƙwayar cutar a jikin matafiya. • Waɗansu mutane da suka zo kusa da matafiyan ma sun kamu ta wajen su. • Akwai yiyuwa cewa wasu wurare za su samu waɗanda za su kamu da COVID-19. • Amma dai akwai abubuwa da yawa da bamu sani ba game da wannan sabuwar ƙwayar cuta, har yanzu muna iya hana cutar kuma mu dakatar da yaɗuwar ta. 3
Ta yaya take yaɗuwa? • Mafi yawancin mutane suna kama cutar daga wasu mutane. • Wataƙila tana yaɗuwa kamar yadda mura da sanyi ke yaɗuwa – ta ƙananan ɗigo waɗanda suke fitowa idan muna magana, tari da atishawa. • Mutane na iya kamuwa idan wannan ɗigon ya shiga hanci, idanuwa ko baki. • Taɓa gurbattatun abubuwa na iya saka ɗigon a hannayen ka. Idan ka taɓa fuskarka sai ɗigon su shiga hancinka/ idanuwanka / bakin ka. 4
Wasu hanyoyin yaɗuwa • Asali wataƙila ƙwayar cutar na yaɗuwa daga "rumbu" a cikin kasuwar dabbobi masu rai ta Wuhan, zuwa mutane. Wasu ƙwayoyin cuta na coronabirus sannane na yaduwa daga jikin dabbobi. o Cutan huhu na ƙasashen larabawa wato Middle East Respiratory Syndrome Coronavirus (MERS-Co. V) daga raƙumai. o Ciwon huhu mai tsanani wato Severe Acute Respiratory Syndrome (SARS) daga dabbar civet. Wannan ƙwayar cutan bata yawo a yanzu. • Wasu ƙwayoyin cuta na coronabirus na yaɗuwa ta kashi, kuma wata ƙila COVID 19 na yaɗuwa haka. 5
Alamomin na farawa kamar sauran cututtuka Zazzaɓi Ciwon makogoro Tari Yankewar numfashi Alamomin na farawa bayan kwana ɗaya da kamuwa, amma zai iya daukar har kwanaki 14. Wasu mutane basu nuna alama, mafi yawanci suna da ciwo mara tsanani. Yana iya zama da tsanani kuma ya kai har ga rasa rai. 6 Ciwon tsoka Zawo
Gane cutar da kulawa Don alamomin na kama da wasu cututtuka da yawa, ana bukatan gwaji don gane cutar (gwajin yawu a makogoro, gwajin jini). Babu wani kulawa ta musamman ta magance wannan cutar. Ana iya magance ciwon mara tsanani don rage zazzaɓin, ko sauƙaƙa zafin ciwo. Idan alamomin ciwon yafi tsanani, dole kulawar ta zama a asibiti. 7
Domin kare COVID-19 Kula da tsaftar kai 8 • Wanke hannaye akai-akai da sabulu da ruwa. • Yi amfani da man tsaftace hannu mai sinadari idan babu sabulu da ruwa a kusa. • Ka guji taɓa fuskar ka (idanuwanka, hanci da baki).
Guji zama ba kariya • Ka nisanci mutane marasa lafiya – kada ka bari suyi tari da atishawa a kanka. • Kada ka raba abinci, abun sha da abubuwanka na kan ka. • Guji ayyukan da akwai yiyuwar za ka kusanci mutane da yawa. 9
Wasu hanyoyin kariya • Kada ka ziyarci kasuwannin ɗanƴen kaya, ko gidajen gona. • Guji taɓa dabbobi kai tsaye (masu rai ko mattatu) da kuma muhallin su. Kada ka taɓa wuraren da ake tsammani ya gurbace da kashi. • Guji taba dabbobin da bana kowa ba - muzuru, karnuka, ɓeraye, tsuntsaye da jemage. • Ka tabbata ka dafa kowane abincin da ya shafi dabobbi (nama, ƙwai) da kyau kafin ka ci. • Rigakafin mura zai taimaka ma hadarin muran yanayi kuma zai yiwu ya kawo rikicewar alamomin COVID -19. 10 Babu hujja a yanzu cewa dabbobin gida
Dubawa da bibiyan waɗanda suka zo kusa da masu cuta Yana da muhimmanci a yanke yaɗuwar ƙwayar cutar • • 11 Za a iya "Duba" mutane a mashigar gari da wurare domin gane mara lafiya. Wataƙila zaʻa tambaye ka daga wajen da kake, kuma zaʻa ɗauki yanayin zafin jikin ka. Hukumomin kiwon lafiya na iya "bibiyar mutane" - don gane mutanen da suka zo kusa da mutumin da yake da COVID-19. Za a iya tambayar "mutanen nan" o su zauna a gida har tsawon kwana sha huɗu (14) saboda kada su ba sauran mutanen cutar. o don sa ido akan lafiyar su har kwanaki 14 ko za su nuna wata alamar cutar. Ka bi shawarwarin hukumomin kiwon lafiya.
Me zaka yi idan ka fara rashin lafiya • Kada ka yi tafiya • Rufe bakin ka idan kana tari da atishawa yi amfani da tsumma ko abun rufe fuska idan akwai - kuma ka wanke hannayen ka da sabulu da ruwa. • Ka nemi shawarar likita – Ka faɗawa likitan wajenda ka je, kuma ko ka zo kusa da mutum mara lafiya. • Idan baka buƙatar zuwa asibiti - zauna a gida har tsawon yadda zaka iya. Kada ka je wajen aiki. Rage hulda da wasu mutane har sai ka warke gabaɗaya. 12
Ƙarin bayani akan COVID-19 Ka riƙa bin labarai da bayanai daga https: //pandemic. internationalsos. com/2019 -ncov 13
Akwai wasu tambayoyi Rashin ɗaukar Alhaki: An samar da wannan ne domin ilimantarwa kawai. Kuma ba don maye gurbin shawarwarin likita ba. Idan ka na da tambayoyi ko damuwa game da batun da aka yi bayani anan, dan Allah a nemi shawara daga masana. © 2020 AEA International Holdings Pte. Ltd. An kare haƙƙin mallaka.
- Slides: 14